1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An nada sabon babban hafsan sojan Kenya

Suleiman Babayo MAB
May 2, 2024

Laftanar Janar Charles Muriu Kahariri ya zama babban habsan sojojin kasar Kenya, yayin da ita kuma Manjo-Janar Fatuma Gaiti Ahmed ta zama mace ta farko da za ta jagoranci rundunar sojan saman kasar.

https://p.dw.com/p/4fRbZ
Shugaba William Ruto na Kenya
Shugaba William Ruto na KenyaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

An nada Laftanar Janar Charles Muriu Kahariri a matsayin sabon babban habsan tsaron kasar Kenya, inda ya gaji tsohon babban hafsan Marigayi Francis Omondi Ogalla da ya rasu sakamakon hadarin karamin jirgin sama mai saukan ungulu tare da wasu hafsoshin soja guda 10.

Shugaba William Ruto ya bayyana sunan Laftanar Janar Charles Muriu Kahariri mai shekaru 62 da haihuwa, wanda yake rike da mukamun mataimakin babban habsa, inda yanzu aka daga-likafansa zuwa babban habsan tsaron kasar. Sannan Shugaba Ruto ya nada Manjo-Janar Fatuma Gaiti Ahmed a mastayin mace ta farko wadda za ta jagoranci rundunar sojan saman kasar ta Kenya.