1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Za a gudanar da bincike kan gano kabaruruka a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
May 11, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan wasu manyan kabaruruka na fararen hula da aka gano a Gaza.

https://p.dw.com/p/4fkND
Gazastreifen I Lage in Rafah
Hoto: Sais Khatib/AFP

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da kwakkwaran bincike a kan rahoton ramukan makare da fararen hula a Zirin Gaza da Khan Younis.

Ramukan an gano su ne makare da daruruwan gawawaki kusa da asibitin Naseer a Khan Younis da kuma wani a kusa da babban asibitin Al-Shifa da ke Gaza a makwannin baya-bayan nan.

A sanarwar ta ofishin Majalisar Dinkin Duniya, ta ce akwai bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa domin daukar matakin hukunta duk wanda aka kama da laifin taka dokokin kasa da kasa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake samun rahoton gano manyan ramuka da gawawakin fararen hula a Gaza ba, wanda kuma ake zargin sojojin Isra'ila, sai dai ko a wannan karon dakarun na Isra'ila sun musanta zargin da ake yi musu.